17 Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba.Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.
18 Abishai, ɗan'uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa'ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku.
19 Shi ya fi shahara daga cikin su talatin ɗin, don haka ya zama shugabansu, amma bai kai su uku ɗin can ba.
20 Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.
21 Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin.
22 Abubuwan da Benaiya, ɗan Yehoyada ya yi ke nan. Da haka ya samar wa kansa suna tare da jarumawan nan talatin.
23 Ya shahara cikin jarumawan nan talatin, amma bai kai su uku ɗin can ba. Dawuda kuwa ya maishe shi ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.