19 Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa'an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra'ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.
20 Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa.
21 Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra'ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.
22 Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.
23 Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24 Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?
25 Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”