21 Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al'amura domin ka sa in san su.
22 Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah.
23 Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar.
24 Ka zaɓar wa kanka jama'ar Isra'ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
25 “Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka.
26 Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.’ Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka.
27 Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a a gare ka.