1 Bayan haka kuma sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar.
2 Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.
3 Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.
4 Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.
5 Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000).
6 Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.