5 Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da 'ya'yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”
6 Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.”'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.
7 Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.
8 Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan 'ya'yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.”
9 Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?
10 Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.”
11 Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.