9 Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?
10 Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.”
11 Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.
12 Yehu kuma ya fita zai tafi Samariya. A hanya, sa'ad da yake a Bet-eked ta makiyaya,
13 sai ya sadu da 'yan'uwan Ahaziya Sarkin Yahuza, sai ya ce, “Ku su wane ne?”Sai suka amsa, “Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, mun zo mu gai da 'ya'yan sarki ne da 'ya'yan sarauniya.”
14 Yehu kuwa ya ce, “Ku kama su da rai.” Sai suka kama su da rai, suka karkashe su a ramin Bet-eked, su arba'in da biyu ne, ba a rage ko ɗaya a cikinsu ba.
15 Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?”Yehonadab ya amsa, “I.”Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.