16 Suka kama ta, suka fitar da ita ta ƙofar dawakai zuwa gidan sarki, can suka kashe ta.
17 Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama'a, yadda za su zama jama'ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama'a.
18 Sai dukan jama'ar ƙasa suka tafi haikalin Ba'al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagaden.Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,
19 ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama'ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna.
20 Dukan jama'ar ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya huta bayan da an kashe Ataliya a gidan sarki.
21 Jowash yana da shekara bakwai sa'ad da ya ci sarauta.