5 Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.
6 Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.
7 Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.
8 Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
9 Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.
10 A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta.
11 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat.