9 Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da 'yan'uwansu.
10 Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin 'ya'yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek.
11 Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana.
12 Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron.
13 Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.
14 Ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffofin gumakan, sa'an nan ya rufe wurarensu da ƙasusuwan mutane.
15 Yosiya ya kuma rushe bagaden da yake a Betel, wanda Yerobowam ɗan Nebat ya gina, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi, tare da tudun, ya farfashe duwatsun, ya niƙe su, sun zama gari, ya kuma ƙone Ashtoret.