19 Sa'an nan Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, ni kuwa in kai ku wurin mutumin da kuke nema.” Sai ya kai su Samariya.
20 Da shigarsu Samariya, sai Elisha, ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan su gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanunsu, suka gani, ashe, suna tsakiyar Samariya ne.
21 Da Sarkin Isra'ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”
22 Amma Elisha ya ce, “Ba za ka karkashe su ba. Ba za ka karkashe waɗanda ba kai ka kama su ta wurin takobinka ko bakanka ba. Ka ba su abinci da ruwa su ci su sha, su koma wurin shugabansu.”
23 Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa'ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara kai wa ƙasar Isra'ila hari ba.
24 Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi.
25 Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.