7 Sa'an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
8 Wata rana, sa'ad da Sarkin Suriya yake yaƙi da Isra'ila, sai ya shawarci fādawansa, suka zaɓi wurin da za su kafa sansani.
9 Amma Elisha ya aika wa Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka yi hankali, kada ka wuce wuri kaza, gama Suriyawa suna gangarawa zuwa can.”
10 Sarkin Isra'ila kuwa ya aika zuwa wurin da Elisha ya faɗa masa. Da haka ya riƙa faɗakar da shi, har ya ceci kansa ba sau ɗaya, ba sau biyu ba.
11 Zuciyar Sarkin Suriya kuwa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan al'amari, don haka ya kirawo fādawansa, ya ce musu, “Wane ne wannan da yake cikinmu, yana goyon bayan Sarkin Isra'ila?”
12 Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A'a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra'ila, yake faɗa wa Sarkin Isra'ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”
13 Sai ya ce, “Ku tafi, ku ga inda yake don in aika a kamo shi.” Aka faɗa masa, cewa a Dotan yake.