12 Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?”Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”
13 Hazayel kuwa ya ce, “Ni wane ne? Ina na sami wannan iko? Ni ba kome ba ne.”Elisha ya amsa ya ce, “Ubangiji ya nuna mini za ka zama Sarkin Suriya.”
14 Sa'an nan Hazayel ya tashi daga wurin Elisha ya koma wurin Ben-hadad. Ben-hadad ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa maka?”Sai ya ce, “Ya faɗa mini, cewa lalle za ka warke.”
15 Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa'an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu.Sai ya hau gadon sarautarsa.
16 A shekara ta biyar ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
17 Yana da shekara talatin da biyu da haihuwa sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi shekara takwas yana sarauta a Urushalima.
18 Ya bi halin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri 'yar Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji.