17 Yana da shekara talatin da biyu da haihuwa sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi shekara takwas yana sarauta a Urushalima.
18 Ya bi halin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri 'yar Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji.
19 Duk da haka Ubangiji bai hallaka Yahuza ba, saboda bawansa Dawuda, tun da yake ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa har abada.
20 A zamanin Yoram, Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.
21 Sa'an nan Yoram ya haye zuwa Zayar tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare da shugabannin karusansa, ya bugi Edomawan da suka kewaye shi, amma sojojinsa suka gudu zuwa alfarwansu.
22 Haka kuwa Edom ta tayar wa Yahuza har wa yau. A lokacin kuma Libna ta tayar wa Yahuza.
23 Sauran ayyukan Yoram da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.