20 A zamanin Yoram, Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.
21 Sa'an nan Yoram ya haye zuwa Zayar tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare da shugabannin karusansa, ya bugi Edomawan da suka kewaye shi, amma sojojinsa suka gudu zuwa alfarwansu.
22 Haka kuwa Edom ta tayar wa Yahuza har wa yau. A lokacin kuma Libna ta tayar wa Yahuza.
23 Sauran ayyukan Yoram da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
24 Yoram kuwa ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.
25 A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
26 Ya ci sarauta yana da shekara ashirin da biyu da haihuwa, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikanyar Omri, Sarkin Isra'ila.