20 Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”
21 Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel.”
22 Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?”Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?
23 Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!”
24 Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa.
25 Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa,
26 ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”