23 Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!”
24 Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa.
25 Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa,
26 ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
27 Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.
28 Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.
29 Ahaziya ya ci sarautar Yahuza a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Yehoram ɗan Ahab.