7 Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Gaza ta ƙone kagararbirnin.
8 Zan kawar da masu sarautar biranenAshdod da Ashkelon,Zan karɓe sandan mulkin Ekron.Sauran Filistiyawa da suka ragukuma,Za su mutu duka.”
9 Ubangiji ya ce,“Mutanen Taya sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe mutanen sun kaiƙasar Edom.Suka karya yarjejeniyar abuta waddasuka yi.
10 Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Taya,Ta ƙone kagarar birnin.”
11 Ubangiji ya ce,“Mutanen Edom sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun farauci 'yan'uwansu,Isra'ilawa,Suka ƙi su nuna musu jinƙai.Ba su yarda su huce daga fushinsuba.
12 Saboda haka zan aukar da wuta akan Teman,Ta ƙone kagarar Bozara.”
13 Ubangiji ya ce,“Mutanen Ammon sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don haɗamarsu ta ƙasa,Suka tsaga mata masu ciki aGileyad.