15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunacinagarta,Ku yi adalci cikin majalisaralƙalanku!Watakila Ubangiji Allah MaiRundunaZai yi wa sauran da suka ragu nawannan al'umma alheri.
16 Haka Ubangiji Allah Mai Rundunaya ce,“Za a yi kuka, a yi kururuwa atitunan birninku saboda azaba.Daga ƙauyuka za a kirawomutaneSu zo su yi makokin.Waɗanda suka mutu, tare da masumakoki da aka ijarar da su.
17 Za a yi kuka ko'ina cikin dukangonakin inabinkuGama zan zo in yi muku horo.”
18 Taku ta ƙare, ku da kuke marmarinzuwan ranan nan ta Ubangiji!Wane amfani wannan rana za ta yimuku?Rana ta baƙin ciki ce,Ba ta murna ba.
19 Zai zama kamar wanda ya tsere wazakiYa fāɗa a bakin beyar!Ko kuwa kamar wanda ya komogida,Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.
20 Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.
21 Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!