8 Zan yi gāba da mutumin nan, zan sa ya zama abin nuni, da abin karin magana, in datse shi daga cikin mutanena, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.
9 “Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra'ila.
10 Za su ɗauki alhakin hukuncinsu, wato hukuncin annabin, da hukuncin mai yin roƙonsa duk ɗaya ne,
11 don kada mutanen Isra'ila su ƙara rabuwa da ni, ko kuma su ƙara ƙazantar da kansu ta wurin laifofinsu, amma za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”
12 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
13 “Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,
14 ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.