34 Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da yake ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”
35 Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.
36 “Ubangiji Allah ya ce, da yake kunyarki ta bayyana, an buɗe tsiraicinki cikin karuwancinki, saboda kuma gumakanki, da jinin 'ya'yanki da kika miƙa wa gumakanki,
37 domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.
38 Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.
39 Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.
40 “Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu.