25 “Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?
26 Sa'ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa.
27 Idan kuma mugu ya bar muguntarsa da yake yi, ya kuwa bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu.
28 Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba.
29 Amma mutanen Isra'ila suna cewa hanyar Ubangiji ba daidai ba ce. Ya mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?
30 “Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.
31 Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila?