7 wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,
8 wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama,
9 wanda yake bin dokokina, yana kuma kiyaye ka'idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.
10 “Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan'uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, [ko shi kansa,
11 bai yi irin waɗannan abubuwa ba,] wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa,
12 yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,
13 yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.