19 Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da yake dukanku kun zama ƙwan maƙera zan tattara dukanku a Urushalima.
20 Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da darma, da kuza a cikin tanderu, su hura wuta a kansu, don su narkar da su, haka zan tattara ku da zafin fushina in narkar da ku.
21 Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta.
22 Kamar yadda azurfa takan narke a cikin tanderu, haka kuma za ku narke, za ku sani ni, Ubangiji ne, na zubo muku da zafin fushina.”
23 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
24 “Ɗan mutum, ka ce mata, ‘Ke ƙasa ce marar tsarki, wadda ba a yi ruwan sama a kanki ba a lokacin da na yi fushi.’
25 Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu.