25 Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama 'ya'yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta.
26 Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.
27 Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.
28 “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.
29 Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.
30 Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al'umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu.
31 Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”