26 Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.
27 Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.
28 “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.
29 Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.
30 Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al'umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu.
31 Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”
32 Ubangiji Allah ya ce,“Za ki sha babban hukuncin da 'yar'uwarki ta sha,Za a yi miki dariya da ba'a,Gama hukuncin yana da tsanani.