4 Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
5 Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,
6 waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu.
7 Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.
8 Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin 'yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta.
9 Domin haka na bashe ta a hannun kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.
10 Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama 'ya'yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa'ad da aka hukunta ta.