18 Yanzu tsibiran za su yi rawar jiki a ranar faɗuwarki.Ji, tsibiran teku za su gigice saboda shuɗewarki.’ ”
19 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Sa'ad da na maishe ki kufai kamar biranen da ba a zauna cikinsu ba, sa'ad da kuma na dulmuye ki cikin zurfin teku,
20 sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.
21 Zan sa ki yi mummunan ƙarshe, ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a same ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa!”