3 domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.
4 Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan'kare ƙasarta, in maishe ta fā.
5 Za ta zama wurin shanya taruna a tsakiyar teku. Za ta kuma zama ganima ga sauran al'umma. Ni Ubangiji na faɗa.
6 Ya'yanta mata waɗanda suke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”
7 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.
8 Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.
9 Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.