1 Sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ya kai ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.
3 Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce,‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!
4 Teku ta kewaye kan iyakarki,Maginanki sun ƙawata ki.
5 Sun yi katakanki da itacen fir na Senir,Sun sari itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6 Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.