7 Don haka zan tura baƙi a kanka,Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al'umma.Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka,Za su ɓara darajarka.
8 Za su jefar da kai cikin rami,Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.
9 Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?
10 Za ka yi mutuwa irin ta kare ta hannun baƙi,Gama ni Ubangiji Allah na faɗa.’ ”
11 Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,
12 “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce,‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!
13 Kana cikin Aidan, gonar Allah.An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja,Tare da zinariya.Kana da molo da abin busa.A ranar da aka halicce kaSuna nan cikakku.