24 Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida.
25 Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama'a.
26 Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su 'yan tawaye ne.
27 Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”