23 Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya.
24 Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali.
25 Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar.
26 Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in warwatsa su a ƙasashen duniya. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”