3 Gama ranar ta gabato,Ranar Ubangiji ta yi kusa,Rana ce ta gizagizai,Ranar halakar al'ummai.
4 Takobi zai fāɗa a kan Masar,Azaba kuma za ta sami Habasha.Za a kashe mutane a Masar,Za a kwashe dukiyarta,A rushe harsashin gininta.
5 “Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”
6 Ubangiji ya ce,“Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi.Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.
7 Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe,Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.
8 Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji,Sa'ad da na kunna wuta cikin Masar,Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.
9 “A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”