18 “Ɗan mutum, ka yi kuka saboda jama'ar Masar. Ka tura su tare da sauran al'umma zuwa lahira wurin waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.
19 Ka ce, ‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.’
20 “An zare takobi don a kashe jama'ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi.
21 Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’
22 “Assuriya tana can da dukan taron jama'arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi.
23 An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama'arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.
24 “Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.