1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,
3 idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama'ar.
4 Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa.
5 Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.