1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,
3 idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama'ar.
4 Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa.
5 Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.
6 Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’