9 Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”
10 “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’
11 Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’
12 “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.
13 Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.
14 Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,
15 idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.