13 Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.
14 Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”
15 Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
16 “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’
17 Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.
18 Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,
19 sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.