13 Daga bayan rufin ɗaya ɗakin 'yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar.
14 Ya yi ginshiƙai kamu sittin. Akwai ɗakuna kewaye da shirayin da yake bakin ƙofa.
15 Daga gaban ƙofar shiga, zuwa kurewar shirayi na can ciki kamu hamsin ne.
16 Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.
17 Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen.
18 Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da yake ƙasa ƙasa.
19 Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.