18 Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da yake ƙasa ƙasa.
19 Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.
20 Ya kuma auna tsayin ƙofar arewa da faɗinta wadda take fuskantar filin waje.
21 Tana da ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe. Girman ginshiƙanta da shirayinta, daidai suke da ƙofa ta fari. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.
22 Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki.
23 Fili na ciki yana da ƙofa daura da ƙofar arewa da ta gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.
24 Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran.