34 Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Tana da matakai takwas.
35 Sa'an nan kuma ya kai ni ƙofar arewa, ya auna ta. Girmanta daidai yake da na sauran.
36 Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.
37 Ginshiƙai suna fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Ita ma matakanta takwas ne.
38 Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa take duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa.
39 A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi.
40 Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar.