1 Sai ya kai ni cikin Haikalin, sa'an nan ya auna ginshiƙai. Fāɗin ginshiƙan kamu shida ne a kowane gefe.
2 Fāɗin ƙofar kamu goma ne. Madogaran ƙofar kamu biyar ne a kowane gefe. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu arba'in ne faɗinsa kuma kamu ashirin ne.
3 Sai ya shiga ɗaki na can ciki, ya auna madogaran ƙofar, ya sami kamu biyu biyu. Tsayin ƙofar kuma kamu shida ne. Faɗin ƙofar kamu bakwai ne.
4 Ya kuma auna ɗaki na ƙurewar ciki, tsawonsa kamu ashirin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”
5 Sai kuma ya auna bangon Haikalin, kaurinsa kamu shida ne. Faɗin ɗakunan da suke kewaye da Haikalin kamu huɗu ne.