1 Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda take wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe.
2 Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe.
3 Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”
4 Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki.
5 Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.
6 “Ka ce wa 'yan tawaye, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Ku daina ayyukanku na banƙyama.
7 Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.