6 Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra'ila duka.”
7 “Ƙasar da take a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas.
8 Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra'ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra'ila ƙasar bisa ga kabilansu.”
9 “Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra'ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari'a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.
10 “Sai ku kasance da ma'aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.
11 “Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.
12 “Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”