1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra'ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!
3 “Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki.
4 Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”
5 Ubangiji Allah ya ce, “Masifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa!
6 Matuƙa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi!
7 Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.