4 Ya ce masa, “Ka ratsa cikin birni, wato Urushalima, ka sa shaida a goshin mutanen da suke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin.”
5 Na kuma ji ya ce wa sauran, “Ku bi shi, ku ratsa cikin birnin, ku kashe, kada ku yafe, kada kuwa ku ji tausayi.
6 Ku kashe tsofaffi, da samari, da 'yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda yake da shaida. Sai ku fara a Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da suke a gaban Haikalin.
7 Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa'an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da suke cikin birnin.
8 Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”
9 Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’
10 Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”