5 Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran.Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana,
6 Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar.
7 Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
8 Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.
9 Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.
10 A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.
11 Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,