6 Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.
7 “Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.
8 Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”
9 Allah kuma ya ce wa Ibrahim, “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, da kai da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu.
10 Wannan shi ne alkawarina da za ka kiyaye, da kai da zuriyarka a bayanka. Sai a yi wa kowane ɗa namiji kaciya.
11 Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku.
12 Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.