12 Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.”
13 Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”
14 Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.
15 Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su,
16 fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi.
17 Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya.
18 Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.”Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?”