15 Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”
16 Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”
17 Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.”
18 Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al'amudi, ya kuwa zuba mai a kan al'amudin.
19 Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz.
20 Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa,
21 har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna,